Babu dokar da ta hana gurfanar da kananan yara a Najeriyar- ministan shari'a

Babu dokar da ta hana gurfanar da kananan yara a Najeriyar- ministan shari'a

Ministan shari'ar na Najeriya ya bayyana wannan hakan ne bayan da gwamnatin shugaba Tinubu na ƙasar ta ba da umarnin  a saki yaran da aka gurfanar dasu a gaban ƙuliya wadda a cikinsu aka samu wadanda suka riƙa suma a kotu, abin da ya haifar da cece-kuce a ƙasar.

Da yake bayani a ranar Alhamis a Abuja babban birnin ƙasar yayin kaddamar da sabon ginin ofishin harkokin shari’a wato Law Corridor da kuma gabatar da wani littafi kan tsarin shari’ar Najeriya a zamanance, ministan shari’ar ya bayyana cewa, gurfanar da kananan yaran na cikin dokar Najeriya.

Inda yake cewa "Babu wata doka a kasar nan da ta ce ba za a iya yi wa kananan yara shari'a ba.

Fagbemi yayi wannan magana ce a daidai lokacin da ‘Yan Najeriya da kungiyoyin kasa da kasa suka yi Allah-wadai da shari’ar masu zanga-zangar 119 da suka hada da kananan yara ƴan tsakanin shekaru 14-17.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)