A hukuncin da kotun ɗaukaka ƙarar ta yanke ta ce babbar kotun jihar Kano ce kaɗai ke da hurumin sauraron ƙarar da ta shafi masarautar ta jihar.
Alƙalin da ya jagoranci hukuncin mai shari'a Gabriel Kolawole ya ce babbar kotun tarayya da ke Kano bata da hurumin yanke hukunci kan sha'anin sarauta a Kano, inda ya umarci a mayar da shari'ar zuwa babbar kotun jihar saboda ita ta dace ta saurari ƙarar.
Sauran alƙalai biyu da suka saurari shari’ar sun amince da ra'ayin mai shari'a Kolawole kan cewa babbar kotun tarayya a Kano bata da hurumin sauraron shari’ar masarautar jihar.
Sai dai alƙalan biyu basu amince da ra'ayin cewa a mayar da ƙarar ga babban mai shari'a na Kano domin tura batun gurin wani alƙalin babbar kotun jiha domin sake sauraron ƙarar ba, maimakon haka alƙalan biyu sun yanke hukuncin rufe shari'ar da ke gaban babbar kotun tarayyar saboda ba ta da hurumin sauraronta.
Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ne ya sake dawo da Muhammadu Sunusi II a matsayin sarkin jihar bayan gwamnatin tsohon gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya tsigeshi a baya.
Gwamnan Abba ya kuma rushe ƙarin masarautu da gwamnatin Ganduje ta samar da suka haɗa da Bichi da Rano da Gaya da Ƙaraye.
To sai dai bayan dawo da shi kan karaga aka fara wata sabuwar dambarwa a jihar bisa yadda sarkin Kano Aminu Ado Bayero da aka tsige ya dawo jihar tare da tarewa a gidan sarki na Nasarawa.
Daga nan ne kuma aka shiga shari’ar ƙalubalantar tsigeshi da gwamnan jihar Abba Kabir Yusuf ya yi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI