Babban Hafsan sojin Najeriya Lagbaja ya rasu ya na da shekaru 56

Mai bai wa shugaban ƙasa shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai Bayo Onanuga ne ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa ranar Laraba.

“Shugaba Bola Ahmed Tinubu, Babban Kwamandan Sojoji, na nadamar sanar da Rasuwar Laftanar Janar Taoreed Abiodun Lagbaja, Shugaban Hafsan Sojin ƙasa yana da shekaru 56.”

Babban hafsan rikon kwarya

Hakan na zuwa ne kwanaki bayan da shugaban ƙasa Bola Tinubu ya naɗa Manjo Janar Olufemi Olatubosun a matsayin babban hafsan sojin ƙasa na riko har zuwa lokacin da Laftanar Janar Taoreed Abiodun Lagbaja zai dawo bakin aikinsa, wanda tun farko aka ce yana kwance a asibiti saboda fama da jinya, biyo bayan cece kuce dangane da halin da Janar Lagbaja ke ciki a makon jiya.

Janar Olatubosun mai shekaru 56 abokin karatun Lagbaja ne kamar yadda sanarwar ta gabatar.

Raɗe-raɗin mutuwar Lagbaja.

Hakan na zuwa ne bayan raɗe-raɗin cewa hafsan sojan ya rasa ransa a sakamakon cutar daji.

Wasu daga cikin kafafen yaɗa labarai na cikin gidan ƙasar ne suka fara ruwaito labarin cewa hafsan sojan ya rasa ransa a ƙasar waje, a sakamaon jinyar cutar kansa ko kuma daji, batun da nan take shalkwatar tsaron ta musanta, tana mai cewa tabbas jagoran na sojoji yana ƙasar waje ƙarkashin kulawar likitoci amma yana nan da ransa.

Jim kaɗan bayan sanarwar da ta yi watsi da labarin mutuwar ne kuma, wata sabuwa ta sake ɓulla da ke cewa shalkwatar tsaron ta yi sabon naɗin rikon kwarya a mukamin na Laftanar Kanar Lagbaja.

Ta cikin wata sanarwa da daraktan yaɗa labaran shalwakatar tsaron, Birgediya Janar Tukur Gusau ya fitar, ta ce babu wani dalili dai zai sa a naɗa mai rikon kwarya a muƙamin na Laftanar Lagbaja, saboda kawai yaje a duba lafiyarsa a wani ɓangare na hutunsa na shekara.

Takaiceccen tarihin Lagbaja

“An haifi Laftanar Janar Lagbaja a ranar 28 ga watan Fabrairun shekarar 1968, wanda shugaba Tinubu ya naɗa a matsayin babban hafsa a ranar 19 ga watan Yuni, 2023.

A shekarar 1987, ya shiga makarantar horas da sojoji ta Najeriya, kuma a ranar 19 ga watan Satumbar 1992 ya fito da muƙumin laftanar na biyu a rundunar sojin Najeriya.

A tsawon aikinsa, Laftanar Janar Lagbaja ya nuna kyakkyawan jagoranci da jajircewa, inda ya yi aiki a matsayin kwamandan runduna ta 93 da kuma bataliya ta 72 na musamman.

Ya taka rawar gani ayyukan tsaron cikin gida da dama da suka hada da Operation ZAKI a jihar Binuwai da Lafiya Dole a Borno da Udoka a Kudu maso Gabashin Najeriya, da Operation Forest Sanity a jihar Kaduna da Neja.

Ya halarci kwalejen koyon dabarun yakin na  Amurka, inda ya samu digirin digirgir a fannin Dabaru da shugabancin soja.

Lt. Janar Lagbaja ya rasu ya bar matar sa Mariya da ‘ya’yansu biyu.

Shugaba Tinubu ya jajantawa iyalansa da sojojin Najeriya a wannan mawuyacin lokaci. Ya yi wa Laftanar Janar Lagbaja addu’ar yafiya tare da karrama gagarumar gudunmawar da ya bayar ga al’umma.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)