Tinubu yace abin kataici ne yadda Najeriya ke da tarin yawan dabbobi amma kuma bata cin gajiyarsu yadda ya dace kamar yadda ake gani a wasu kasashen duniya.
Shugaban wanda ya jagoranci wani taron tintiba a kan yadda za'a inganta kiwon dabbobi a fadarsa, yace lura da alkaluman dake nuna cewa Najeriya na da dabbobin da suka hada da kaji miliyan 563 da shanu miliyan 58 da awaki miliyan 124 da raguna miliyan 60 da kuma aladu miliyan 16 ya dace kasar ta dinga cin moriyarsu fiye da yadda ake gani yanzu.
Wadannan wasu shanu ne da ake kwionsu a kasar Brazil dake samar da nono mai yawa AFP - MAURO PIMENTEL
Tinubu yace rashin kular da aka samu a shekarun baya ya taimaka wajen koma bayan da aka samu wajen karancin madarar da naman da ake samarwa, abinda ya yi dalilin kashe tsakanin dala biliyan guda da miliyan 200 zuwa dala biliyan guda da rabi wajen shigo da su daga kasashen ketare.
Shugaban ya ce wannan ne dalilin da ya sa ya kaddamar da kwamitin da ya bada shawarar kafa ma'aikata ta musamman da za ta mayar da hankali a kan wannan bangare a watan Yulin da ya gabata domin nazari da kuma bada shawarwarin hanyoyin da za'a bi domin inganta kiwo a Najeriya.
Tinubu ya ce fatarsu itace inganta harkar noma da kiwo ta hanyar da za'a samu zaman lafiya da fahimtar juna a tsakanin masu wadannan sana'oi ta yadda kasa za ta ci gajiyarsu.
Shugaban Najeriya Bola Tinu da Farfesa Attahiru Jega © Nigeria PresidencyShugaban ya ce Najeriya ba zata ci gaba da dogara da kasashen ketare wajen samarwa jama'arta abinci da kuma naman da za su ci ba, saboda haka gwamnatinsa ta mayar ad hankali a kan wadanan bangarori masu muhimmanci ga ci gaban kasa tare d asamar da ma'aikata ta musamman a kai.
Tinubu ya yabawa tsohon gwamnan Kano Abdullahi Ganduje da mai bai wa shugaban kasa shawara a kan harkokin tsaro Malam Nuhu Ribadu da kuma Farfesa Attahiru Jega a kan rawar da suka taka wajen samo maslahar samar da wannan ma'aikata.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI