
A wata hira da aka yi da El-Rufai cikin dare ne tsohon gwamnan Kadunan ya yi zargin cewa Nuhu Ribadu yana da burin tsayawa takarar shugaban ƙasa a babban zaɓe mai zuwa.
A yayin hirar da aka yi da shi a cikin dare a kafar Arise TV ranar Litinin, El-Rufai ya bayyana cewa sun raba jiha da tsohon abokin nasa Nuhu Ribadu da kuma Gwamnan Kaduna mai ci kuma magajinsa, Sanata Uba Sani, yanzu duk ba abokansa ba ne.
Amma martaninsa, a cikin sakon da ya fitar jim kaɗan da ta tsohon gwamnan, Nuhu Ribadu ya ce, ƙarya El-Rufai yake yi cewa ya taɓa yin maganar tsayawarsa takarar 2031 da tsohon gwamnan ko da wani.
Ba don kada in yi shiru a ɗauka maganar El-Rufai gaskiya ba ce, da na yi watsi da shi. Ni tulin aikin da ke gabana a yanzu ma kaɗai ya ishe ni, balle in tsaya ɓata lokaci ina cacar baka da El-Rufai ko waninsa a kafofin watsa labarai.
Martanin Nuhu Ribadu ga El-Rufai
Duk da cewa ya sha takala ta da caccaka ta, amma saboda mutunta tsohuwar abotarmu, ban taɓa fitowa na aibata shi ba, kuma ba zan fara ba.
“Amma ina roƙon jama’a su yi watsi da maganganun da El-Rufai ya yi a kaina.
“Domin kawar da shakku, babu mahalukin da na taɓa magana da shi cewa zan nemi takarar shugaban ƙasa a 2031. Abun da na sa a gaba shi ne ganin Najeriya ta bunƙasa da kuma nasarar Gwamnatin Shugaban Ƙasa Bola Tinubu.
“Saboda haka ina roƙon El-Rufai ya ƙyale ni, in fuskanci aikin yi wa kasa hidima da ke gabana, kamar yadda ni ma ban shiga masa harkokinsa ba.
Tinubu ne ya sauya ra’ayi kan ba ni muƙamin Minista — El-Rufai
El-Rufai, ya musanta batun cewa Majalisar Tarayya ce ta ƙi tabbatar da shi domin zama Minista a shekarar 2023.
El-Rufai ya bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu ne ya sauya ra’ayi kan ba shi muƙamin duk da sun ƙulla yarjejeniya a kan hakan.
Ana iya tuna cewa, a watan Agustan 2023 ne Majalisar Dattawa ta ƙi tabbatar da El-Rufai a matsayin Minista, inda ta bayyana dalilai da suka shafi tsaron ƙasa da Hukumar Tsaron Farin Kaya DSS ta ba da shawara.
Sai dai a hirarsa da gidan Talabijin na Arise a ranar Litinin, El-Rufai ya ce duk ba wannan ba ne face Shugaba Tinubu ne ya sauya shawara kan ba shi muƙamin.
A cewarsa, Shugaba Tinubu ne ya sauya masa akalar ƙudirinsa bayan shafe shekaru takwas a matsayin Gwamnan Kaduna.
Bayan shafe shekaru takwas a matsayin Gwamnan Kaduna, ina da wasu burace-burace da na ƙudirta amma Tinubu ya nemi na bayar da gudunmawa a gwamnatinsa.
“Bayan haka ne muka ƙulla yarjejeniyar da sharaɗin cewa zai ba ni muƙamin Minista, amma daga bisani ya sauya shawara.
“Saboda haka a daina yarda da cewa Majalisar Tarayya ce ta ƙi tabbatar da ni saboda ba haka abun yake ba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI