Ba neman kudi ya kawo ni karagar mulkin Najeriya ba - Tinubu

Ba neman kudi ya kawo ni karagar mulkin Najeriya ba - Tinubu

Tinubu ya bayyana haka ne lokacin da tsoffin shugabannin majalisar dokokin kasar suka ziyarce shi a fadarsa dake Abuja, inda ya shaida musu cewar zai ci gaba da jajircewa wajen gabatarwa jama'ar Najeriya romon dimokiradiya ta hanyar gudanar da manyan ayyuka da samar da abinci da makamashi da tsaro da ilimi tare da kuma bunkasa tattalin arzikin kasa.

Shugaban wanda ya yaba da goyan bayan da yake samu daga wasu daga cikin tsoffin shugabannin majalisun ba tare da la'akari da jam'iyyar da suke ba, ya bukace su da su ci gaba da sanya ci gaban kasa da kuma hadin kai a gaba.

Tinubu ya bayyana fatar ganin Najeriya ta shawo kan dimbin matsalolin da suka mata dabaibayi da kuma hana ta ci gaba, inda ya kara da cewar muddin 'yan Najeriya suka hada kansu ba tare da nuna banbanci a tsakanin su ba, kasar na iya magance kalubalen da ake fuskanta kamar yadda wasu kasashen duniya suka yi.

Shugaban ya shaida musu wasu daga cikin matakan da yake dauka da zummar tinkarar wasu daga cikin wadannan matsaloli tare da janyo hankalin shugabannin da su daina korafe korafe wajen mayar da hankali a kan matakan da ya dace a dauka domin gyara.

Yayin jawabinsa shugaban tawagar kuma tsohon shugaban majalisar dattawa Sanata Ken Nnamani wanda ya bayyana cikakkiyar goyan bayansu ga jagorancin shugaba Bola Tinubu, ya jinjina masa dangane da matakan da ya dauka na ceto kananan hukumomi daga kamun kazar kukun da gwamnonin jihohi suka musu.

Nnamani yace suna da yakinin cewar shugaban zai tinkari matsalolin da suka addabi Najeriya bi da bi domin magance su ta hanyar da jama'ar kasar za su samu numfasawa da kuma sanya kasar cikin sahun gaba a kasashen duniya.

Shugaban tawagar yace sun gano yadda wasu fitattun mutanen Najeriya ke sakaci da kuma nuna halin ko in kula dangane da yanayin da kasar ta samu kanta, kuma wannan ne ya sa suka hada kansu domin taimakawa shugaban kasar wajen sauke nauyin dake kansa.

Nnamani yace zasu taimaka masa wajen tinkarar matsalar tattalin arziki da tsaro wadanda za su bude hanyoyin samun arziki a kasa baki daya.

Shugaban tawagar ya kuma yabawa Tinubu wajen nada wasu daga cikin mambobinsu su a muhimman mukamai domin bada gudumawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)