Ba na tsoron mutuwa, amma ina son sulhu - Bello Turji

Ba na tsoron mutuwa, amma ina son sulhu - Bello Turji

A wani sakon bidiyo an jiyo Turji na tabbatar da kashe mai gidansa Halilu Sububu, yayin da ya ce matakin ba zai hana shi magana ba.

Turji ya ce tun lokacin annabawa ake mutuwa, saboda haka ba sa tsoron bama bamai, kuma ba za su daina kisa ba har sai idan an daina kashe musu ƴan uwa a Zamfara da Sokoto da Katsina da kuma Neja.

Yanzu haka Turji wanda ke cikin gaggan ƴan ta'adda 43 da ake nema ruwa  ajallo a yankin arewa maso yammacin Najeriya, ya buƙaci zaman sulhu da gwamnatin Najeriya da ta jiharsa a cikin wani faifen bidiyo mai tsawon minti 5 da dakoki 40.

Ƙasurgumin ɗan bindigar ya ce a shirye yake ya ajiye makamansa muddin gwamnati ta amince da bukatarsa ta zaman tattaunawar sulhu da shi.

A baya-bayan nan rundunar sojin Najeriya ta zafafa ƙaddamar da hare-hare a maɓuyar ƴan ta'adda daban daban a yankin arewa maso yammacin ƙasar da zummar kakkabe su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)