Ƙaramin ministan man fetur na Najeriyar Sanata Heineken Lokpobiri a jawabinsa gaban taron manema labarai bayan wata ganawa da mataimakin shugaban Najeriyar Kashim Shettima da kuma babban daraktan kamfanin man ƙasar NNPC Mele Kyari, ya ce shugaban ƙasar Bola Ahmed Tinubu ya damu matuƙa da matsin rayuwar da al’ummarsa ke fama da ita.
A Talatar makon nan ne kamfanin mai na Najeriyar NNPC ya sanar da matakin ƙara farashin man na fetur zuwa naira 897 kan kowacce lita guda daga farashin naira 617 da ake sayarwa a baya.
Matakin na NNPC wanda a farko gwamnatin Najeriyar ta nesanta kanta da cewa ba ita ta umarce shi da ƙarin ba, tuni ya sake birkita rayuwar ƴan ƙasar waɗanda ke fama da matsi da tsadar rayuwa sakamakon hauhawar kayakin masarufi.
Ministan man na Najeriya ya ce za su yi dukkan mai yiwuwa wajen ganin man ya wadatu a sassan ƙasar sai dai hakan baya nufin gwamnatin ƙasar na da rawar takawa wajen rage farashin.
Yanzu haka a wasu sassa na Najeriyar duk lita guda ta man na haura naira dubu 1 da 200 yayinda hatta a biranen da ke kusa da wajen dakon man farashin man a hannun ƴan kasuwa waɗanda a baya ke sayar da shi naira 690 kan duk lita guda yanzu ya koma 950 zuwa 970.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI