Ba mu da hannu a janye tallafin man fetur a Najeriya - IMF

Ba mu da hannu a janye tallafin man fetur a Najeriya - IMF

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ƴan Najeriya ke zargin IMF da hannu a janye tallafin man fetur ɗin.

A yayin zantawa da manema labarai a wannan Juma'ar a birnin Washington DC na Amurka, Darektan IMF a yankin Afrika, Abebe Selassie ya bayyana matakin shugaba Bola Ahmed Tinubu na janye tallafin man a matsayin batu na cikin gida.

Matakin na cikin gida ne. Ba mu da wani shiri a Najeriya. Rawar da muke takawa ta taƙaita ne kan tattaunawa a kai a kai, kamar yadda muke yi da sauran ƙasashe irinsu Japan ko kuma Birtaniya. Inji Selassie.

Kodayake Selassie ya bayyana cewa, matakin na gwamnatin Najeriya kan janye tallafin man na da nasaba da manufofinta na dogon-zango domin haɓɓaka tattalin arziƙin ƙasar.

IMF ta ce ta lura da irin ƙuncin rayuwar da ƴan Najeriya suka faɗa sakamakon janye tallafin, tana mai shawartar gwamnatin Tinubu da ta samar da hanyoyin rage wa al'umma raɗaɗi.

Shugaba Tinubu ya janye tallafin ne jim kaɗan da shan rantsuwar kama aiki a watan Mayun bara bayan ya samu nasara a zaɓen shugaban ƙasa da aka gudanar.

Jim kaɗan da janye tallafin ne, farashin litar mai da sauraren kayayyaki ya yi tashin goron zabbi a sassan ƙasar.

Har yanzu dai ƴan Najeriya na ci gaba da kokawa kan yadda ake sayar da lita mai a kan naira dubu 1,200 duk kuwa da cewa shugaba Tinubu ya karɓi ƙasar ce a lokacin da ake sayar da lita a kan naira 200.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)