Atiku ya zargi gwamnatin Najeriya da sakaci kan kisan sarkin Gobir

Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, Atiku Abubakar,ya ce sakacin gwamnati da na jami'an tsaro ne suka janyo mutuwar sarkin na Gobir.

Ya ce yin burus da gwamnati ta nuna, da rashin ingantaccen tsari daga jami'an tsaro sun taimaka wajen yaɗuwar irin waɗannan abubuwa na ban takaici a kasar.

''Yana da muhimmanci mu ƙara jaddada wa gwamnati cewa dole ne ta samar da tsaron rayukan jama'a ta yadda mutane ba za su rayu cikin fargabar fusknatar irin haka ba''

Atiku Abubakar ya nuna alhininsa kan rasuwar sarkin tare da miƙa saƙon ta'aziyyarsa ka iyalai da ɗaukacin al'ummar masarautar Gobir, da gwamnatin jihar Sokoto kan mutuwar sarkin da ya bayyana a matsayin mai ''cike da tashin hankali''

Al'umma na sakon jaje game da batun 

Tuni kungiyoyin da ke kisshin al’umma da daidaikun mutane ke cigaba da bayya alhininsu wanda mawaƙin Jam'iyyar APC Dauda Kahutu Rarara ya jajantawa al'ummar Musulmi kan kisan gillar da ƴan ta'adda suka yiwa Sarkin Gobir Alh. Isah Bawa Muhammad.

A wata sanarwa da Rararan ya fitar ta hannun makusancinsa Malam Abdullahi Al-hikima ya ce rashin Sarkin babban rashi ne ga al'ummar Najeriya bakiɗaya ba iya ga iyalansa ba.

Idan ba manta ba a kwanakin bayane masu garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa,sunyi garkuwa da mahaifiyar mawaki Rarara,sai dai ta samu kubuta da ranta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)