Yayin da yake tsokaci a kan bikin cikar Najeriya shekaru 64 da samun 'yancin kai, Atiku wanda ya bayyana farin cikinsa na dorewar dimokiradiya a cikin kasar, yace a karan farko a tarihin Najeriya an samu dogon lokacin da ake tafiyar da mulkin farar hula ba tare da samun targade ba.
Saboda haka, tsohon mataimakin shugaban kasar ya janyo hankalin manyan 'yan siyasar kasar da su tashi tsaye wajen kare mulkin dimokiradiyar da kawar da duk wani yunkuri na mulkin kama karya.
Atiku ya ce bikin da ake yi yau ya biyo bayan hadin kan da shugabannin farko suka yi ne wajen aiki tare na samarwa kasar mulkin kai ta hanyar lumana tare da mikawa wadanda suka biyo bayan su domin jagorancin kasar.
Tsohon mataimakin shugaban ya kuma koka a kan koma bayan da aka samu wajen gudanar da ingantaccen zabe ta yadda wadanda ke karagar mulki ke tafka magudi.
Atiku ya ce yayin da masu mulki ke cin karen su babu babbaka wajen magudin zaben, an bar 'yan adawa a matsayin 'yan kallo wadanda ba su da wani karsashi.
Tsohon shugaban kasar ya bayyana fargabar samun kasa mai jam'iyya daya tilo, wadda za ta hana 'yan adawa rawar gaban hantsi, ya yin da ya janyo hankalin daukacin 'yan siyasa da fitattun 'yan kasa da su tashi tsaye wajen dawo da dimokiradiyar Najeriya a kan hanya mai kyau.
Atiku ya kuma bukaci hadin kan 'yan siyasa daga kowanne bangare da su hada kawance domin samarwa 'yan Najeriya mafita mai karfi da za ta kai kasar tudun mun tsira.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI