Atiku ya buƙaci gudanar da gwamnatin karɓa-karɓa mai wa'adin shekaru 6 sau guda

Atiku ya buƙaci gudanar da gwamnatin karɓa-karɓa mai wa'adin shekaru 6 sau guda

Atiku wanda kuma ya yi wa babbar jam’iyar adawa ta ƙasar PDP takarar shugabancin ƙasa a zaɓen da aka yi a shekarar da ta gabata, ya kuma buƙuci a gyara yadda wa’adi daya na tsaron shekara shida ne shugaban ƙasa zai yi, sabanin wa'adin biyu na shekaru 4-4 da ake yi a yanzu.

Tsohon mataimakin shugaban ƙasar dai ya miƙa buƙatar ce, a wani saƙo da ya aike wa mataimakin shugaban majalisar dattawa, kuma shugaban kwamitin riwa kundin tsarin mulkin ƙasar kwas-kwarima.

A cewarsa, hakan zai kara inganta sha’anin dimukaradiya da aka kwashe sama da shekaru 25 ana bin tafarkinta a ƙasar.

Idan dai ba a manta ba, majalisun Najeriya sun fara zama don yi wa kundin tsarin mulkin ƙasar na shekarar 1999 gyaran fuska, wanda zai shafi gwamnatin karɓa-karɓa da cin gashin kan ƙananan hukumomi da ƙirkirar wasu sabbin jihohi da komawa tsarin gwamnatin shiya da dai sauransu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)