Atiku Abubakar ya sanar da wannan tallafin ne a wata ziyarar jaje da ya kai fadar gwamnatin jihar Barno, lokacin da ya ke ganawa da gwamna Babagana Zulum a Maiduguri wannan Lahadin.
Tsohon shugaban ƙasar ya yi addu’ar Allah ya jikan wadanda suka rasa rayukansu da kuma samun sauki cikin gaggawa ga wadanda suka jikkata da kuma wadanda suka rasa dukiyoyinsu.
Yayin da ziyarci gidan gwamnati da ke Maiduguri ta shi da tawagarsa Atiku ya mika ta’aziyyarsa ga gwamna Zulum da gwamnati da kuma al’ummar jihar, musamman wadanda suka rasa ƴan uwansu.
Baya ga tallafin ƙudi da ya bayar Atiku ya kuma yi kira ga aminansa da sauran abokan huldar sa da su bada tasu gudunmuwarsu wajen ayyukan agajin a Maiduguri0
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI