Atiku da Obi na shirin haɗewa domin kayar da gwamnatin APC a 2027

Atiku da Obi na shirin haɗewa domin kayar da gwamnatin APC a 2027

Mai magana da yawun Atiku Abubakar, Paul Ibe ne ya tabbatar da wannan yunkuri a tattaunawarsa da gidan talabijin na Channels, inda ya ce dukkanin mutum biyu sun ɗauki darasi kan kura-kuran da suka tafka a baya, Suna kuma shirin haɗewa domin kayar da jam’iyyar APC a 2027.

Atiku da Obi sun samu ƙuri’u sama da miliya shida-shida a zaben da Bola Tinubu ya samu nasara da ƙuri’a sama da miliyan 8 a 2023. Wannan ne ya sa masu sharhi ke ganin cewar ƴan takarar biyu sun lalata damar da suke da ita ta samun nasara a zaben da ya gabata.

A baya dai Atiku Abubakar da Peter Obi dukkaninsu mambobin jamiyyar PDP ne kafin daga baya suka raba jamiyyar siyasa kuma kowa ya tsaya takarar shugaban ƙasa.

Ibe ya ce ƴan Najeriya basu cancanci  zama a yanayin da suke ciki ba a wannan lokaci, kuma ana cikin mummunan yanayi a ƙasar da ba’a taba ganin iirinshi, jama’a kuma basu da ƙwarin gwiwa.

Martanin APC

A bangare guda jam’iyyar APC ta ce babu wata haɗaka ta ƴan adawa ko ta Atiku Abubakar da Peter Obi da za ta hana shugaban ƙasa Bola Tinubu samun nasara a zaben 2027.

Daractan yaɗa labarai na jam’iyyar APC ta Najeriya Bala Ibrahim ne ya bayyana haka a tattaunawa da jaridar The Punch.

Ya faɗi haka a matsayin martani ga kalaman Paul Ibe da ya ce Atiku da Obi sun gane kuskuren da suka yi a baya kuma za su haɗe kai domin kawar da gwamnatin APC da ta gaza.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)