Shugaban ƙungiyar Emmanuel Osodeke ne ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce jan ƙafar da gwamnati ke yi gama da lamarin na ƙara mai da hannun agogo baya, wajen sha'anin gudanarwar jami’oin gwamnati a ƙasar.
ASUU ta ce kar al’umma su yi kuka da ita idan ta tsunduma yajin aiki, domin a cewarta matsalolin da ake samu a yanzu game da matsalolinsu daga ɓangaren gwamnati ne.
Daga cikin buƙatun ƙungiyar ta ASUU, akwai buƙukatar kammala cimma matsayar kan yarjejeniyarsu da gwamnati ta shekarar 2009 karkashin shawarwarin da kwamitin Nimi Briggs ya samar a shekarar 2021, da kuma biyan mambobinta albashinsu da aka riki sakamakon yajin aikin watanni 8 da suka yi a shekarar 2022.
Sauran sun haɗa da, samar da tsarin biyan malamai da zai maye gurbin na IPPIS da gwamnatin Najeriya ke amfani da shi wajen biyan ma’aikata a ƙasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI