Ɓarayin wayoyin lantarki sun jefa wasu sassan fadar shugaban Najeriya cikin duhu

Ɓarayin wayoyin lantarki sun jefa wasu sassan fadar shugaban Najeriya cikin duhu

A wata sanarwa da kamfanin rarraba hasken lantarkin Najeriya TCN ya fitar a ranar Juma’a ya bayyana cewa, ɓarayin sun yi kaca-kaca da layin wutar lantarki mai karfin 132KV da kuma igiyoyin karkashin kasa da ke dauke da wutar lantarki zuwa yankin tsakiya da kewayen Abuja, lamarin da ya haddasa katsewar wutar lantarki.

Sannan janar Manajan da ke kula da al’amuran jama’a Ndid Mbah ya bayyana cewa, wayoyin na karkashin kasa masu karfin 132kV da aka lalata, su ne ke isar da wutar lantarkin zuwa tashar rarraba wutar lantarki mai karfin 132kV ta kamfanin na TCN.

An aikata wannan badaƙala a kusa da titin sansanin yawon shakatawa na Menillum Park a Abuja, ya shafi sama da kashi 60% na wutar lantarkin da ke Abuja, yayin da barayin suka kwashe tulin wayoyi wanda hakan ya haifar da  katsewar wutar a sassa daban-daban a birnin.

 

Yankunan da ke fuskantar matsalar wutar lantarkin sun haɗa da Maitama da Wuse da Jabi, sai kuma Lifecamp, da Asokoro da Utako da kuma Mabushi, sai kuma wasu sassan fadar shugaban kasa.

Ta ce tuni aka tura injiniyoyin kamfanin na TCN zuwa wurin da lamarin ya faru domin gyara igiyoyin da aka lalata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)