Bayanai sun ce CBN ya kara yawan tsaba ko kuma takardun kudin da ya ke fitar duk shekara zuwa Naira tiliyan guda da rabi, sai dai duk da hakan tuni wasu yankuna suka fara fuskantar ƙamfar takardun kuɗin.
Tuni dai matsalar ƙarancin ƙudin ta ta’azzara a wasu sassa na Najeriyar musamman yankin arewaci batun da har ya fara shafar hada-hadar kasuwanci manya da ƙanana.
Bankin na CBN ya yi gargaɗin cewa zai hukunta dukkanin bankunan kasuwancin da aka samu da laifin ɓoye takardun na Naira ko kuma karkatar da su zuwa ɓangarorin da basu dace ba.
Akwai dai zargin da ke nuna cewa hatta ɗaiɗaikun ƴan kasuwa na taka muhimmiyar rawa wajen ɓoye takardun ƙudin ko kuma sayen kayan abinci don ɓoye wanda wasu masana ke ganin ya taka muhimmiyar rawa wajen haddasa matsalar ta ƙamfar kuɗi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI