Annobar amai da gudawa ta hallaka mutane 359 a sassan Najeriya

Annobar amai da gudawa ta hallaka mutane 359 a sassan Najeriya

Zuwa yanzu jumullar mutum dubu 10 da 837 suka harbu da cutar ta Cholera ko kuma amai da gudawa a sassan Najeriyar cutar da hukumar yaƙi da cutuka masu yaɗuwa ta NCDC ke cewa fantsamuwarta na da alaƙa da ɗabi’ar jama’a ta shan ruwan sama.

Hukumar NCDC ta ce yanzu haka akwai cutar a jihohin Najeriya 21 inda ta kashe kaso mai yawa na masu fama da ita da suka ƙunshi mutum 134 a Lagos sai 52 a Jigawa kana 46 a Kano sannan 26 a Oyo da wasu 16 a Ebonyi da ƙarin 16 a Adamawa baya ga wasu 13 a Rivers sannan 12 a Katsina kana 10 a Bauchi.

Hukumar NCDC ta ce yanayin masu harbuwa da cutar ta Cholera ya ƙaru da kashi 239 a bana idan an kwatanta da yawan mutanen da cutar ta kashe ko kuma suka yi fama da ita a bara.

Alƙaluman NCDC ya nuna cewa an fi ganin yawaitar masu harbuwa da cutar a watan jiya bayan lafawarta a watannin baya, bayanda ta kashe mutane 87 cikin mutum dubu 1 da 938 da suka harbu haka zalika gwajin da aka yiwa mutane 254 aƙalla mutane 175 aka tabbatar da sun harbu.

Cutar ta Cholera wadda bisa al’ada ake samu a cikin ruwa ko abinci NCDC ta ce cutar kan zauna a jikin mutum na tsawon kwanaki 5 gabanin bayyana dalilin da ya sanya buƙatar kiyayewa tare da tsaftace yanayin cimaka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)