
Rahotanni na cewa, wannan ba shine karon farko da bangaren Boko Haram da Bakura Doro ke jagoranci ke fafatawa da Iswap ba a karamar hukumar Abadam dake tafkin Chadi.
A cewar masanin nan kan harkoki da suka shafi ta’addanci Zagazola Makama, fafatawar bangarorin biyu na baya-bayan nan ya wakana ranar Jumma’ar da ta gabata a wani sansanin mayakan ISWAP dake Toumbun Gini da Toumbun Ali.
A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, Makama ya ce akwai yiwuwar gurmuzun ya faɗaɗa zuwa ƙaramar hukumar Kukawa inda bangaren Boko Haram suka yi kaka gida saboda illar da suka yi wa ISWAP a faɗar ta baya-bayan nan a kan ruwa.
Bangarorin biyu na rikici da juna tun bayan da ISWAP ta ɓalle daga cikin Boko Haram tare da mubaya’a ga ƙungiyar IS a shekarar 2016.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI