'Dan majalisar dattawan dake wakiltar Kebbi ta Kudu, Sanata Garba Musa Mai Doki ya bayyana haka lokacin da ya ziyarci RFI Hausa ya kuma tattauna dangane da irin matsalar tsaron da ta dabaibaye su amma aka kasa kai musu daukin da ya dace domin ganin bayanta.
Sanata Mai Doki yace yau kusan shekara guda ya rubutawa shugaban sojojin kasa Laftanar Janar Taoreed Lagbaja wasika domin gabatar da bukatar ganawa da shi, amma har ya zuwa yau ko amsa bai ba shi ba.
'Dan majalisar dattawan ya yi zargin cewar akwai lokacin da aka hallaka musu matasa 70 a rana guda lokacin da suka je kare garuruwansu daga hari, amma ko jaje gwamnatin Kebbi ko ta tarraya bata aika musu ba, ballanta taimakawa iyalan wadannan matasa.
Sai dai Sanatan ya jinjinawa Babban hafsan tsaron kasa, Laftanar Janar Christopher Musa saboda irin taimakon da yake ba su a duk lokacin da suka gabatar masa wata bukata dangane da matsalar 'yan bindigar da suka addabe su.
Sanata Mai Doki ya ce tabbatar da tserewar mutanen garuruwa sama da 100 a yankin Kebbi ta Kudu saboda fitinar 'yan bindigar, wadanda ke kwashe musu dabbobi da mutane.
Kuna iya sauraron cikakkiyar hirar da Sanata Mai Doki ya yi da RFI Hausa da karfe 5 na yammacin yau. Kuma za'a maimata gobe da karfe 7 na safe.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI