Ana fargabar mutum 12 sun mutu sakamakon wata fashewa a jihar Zamfara

Ana fargabar mutum 12 sun mutu sakamakon wata fashewa a jihar Zamfara

Jaridar Dailytrust ta gano cewa lamarin ya faru da ƙarfe 8 na safiyar yau, bayan wani direban mota da ya kwaso fasinjoji zuwa Dansadau ya tserewa abun fashewar da ƴan bindiga suka dasa.

Wannan ne karo na 2 da aka samu abun fashewa a hanyar Dansadau a cikin wannan mako.

A ranar Lahadin da ta gabata an samu wani abun fashewa da ake zargin an dasa ya ritsa da wata mota ƙirar bus, inda direba dake ciki ya rasa ransa.

Wani mazaunin ƙauyen Yar Tasha da bai amince a ambaci sunanshi ba ya ce, direban motar ƙirar Volkswagen ya afka wurin da abin fashewar yake abinda yayi snadin tarwatsewar motar da yake ciki.

Jami’in dake kula da aikin dakarun Operation Fansar Yamma, Lutanal Kanal Abubakar Abdullahi ya tabbatarwa da kafar talabijin ta Channels faruwar lamarin.

Ya ce a yanzu haka jami’ansu na bibiyar batun don gano irin barnar da aka samu da kuma tabbatar da ganin cewa waɗanda suka aikata laifin sun girbi abinda suka shuka.

Abubakar ya kuma buƙaci alumma su sanya ido kan duk wani motsi da basu gamsu da shi ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)