Wani kwale-kwalen katako mai ɗauke da mutane 70 ne ya kife a yayin da ya ke ƙoƙarin tsallakar da su zuwa gonakinsu a garin Gummi da safiyar Asabar.
Rahotanni sun ce ba tare da ɓata loaci ba mahukuntan yankin suka shirya aikin ceto, inda bayan laluɓe na tsawon sa’o’i 3, aka ceto mutane 6 daga kogin.
Sama da manoma ɗari 9 su ke tsallakawa wannan kogi kulayaumin don isa ga gonakinsu, amma kwale-kwale biyu ne kaɗai ake da su a wannan yankin, lamarin da ke haddasa ɗaukar fasinjoji fiye da kima, kamar yadda wani basaraken yankin ya bayyana.
Jihar Zamfara wanda ayyukan ƴan bindiga daa ke neman iko da albarkatun ƙasa ya yi wa katutu ta kuma fuskanci matsalar ambaliyar ruwa sakamakon mamamkon ruwan sama.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI