
Harin jirgin saman da aka kai kan ƴan ta'addan Lakurawa ya sauka kan alummar wasu ƙauyuka a ƙaramar hukumar Silame ta jihar Sokoto dake arewacin Najeriya
Kauyukan da harin ya shafa sun haɗa da Gidan Sama da Rumtuwa, kuma lamarin ya faru da misalin ƙarfe 7 na safiyar yau Laraba.
Wani mazaunin yankin Silame mai suna Malam Yahya ya ce ƙauyukan na kusa da dajin Surame inda ake zargin maboyar Lakurawa ne da ƴan bindiga.
Wata majiya ta shaidawa Dailytrust cewa sama da mutum 10 ne suka mutu kuma da dama sun jikkata a sakamakon harin jirgin saman yaƙin.
Kawo yanzu babu wata sanarwa daga hukumomin tsaro kan lamarin.
Shugaban ƙaramar hukumar Silame Alh. Abubakar Muhammad Daftarana ya tabbatar da harin inda ya ce suna bincike kan irin barnar da harin jirgin yaƙin ya yi a ƙauyukan.
Al'ummar ƙauyukan na zaune lami lafiya lokacin da jirgin yaƙin ya yi ruwan wuta kan jama'a
Ya yi wuri na tabbatar da adadin mutanen da harin ya kashe ko suka samu raunuka saboda har yanzu muna tattara bayanai
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI