Ana cin zarafin mata kowane bayan minti 10 a Najeriya - Rahoto

Ana cin zarafin mata kowane bayan minti 10 a Najeriya - Rahoto

Rahoton da Cibiyar da ke kula da matan da aka ci zarafinsu a Najeriya SARC ta fitar ya bayyana cewa tsakanin shekarar 2019 da 2025 dinnan, aƙalla manyan mata, da ‘yan mata da ma ƙananan yara daga ƙananan hukumomi 8 dake jihar kaduna sun fuskanci matsalar cin zarafi saboda jinsin su.

Shugabar SARC da ke yankin Kafanchan, Grace Abim ce ta bayyana adadin yayin wani taron horaswa da ofishin ƙungiyar global rights dake kare haƙƙin dan adam a Najeriya ta shirya a birnin Abuja.

Abim ta ƙara da cewa akwai sauran rina a kaba wajen kawo karshen matsalar cin zarafin mata a Najeriya duk kuwa da cewa mutane sun fara fitowa fili don bayyana irin halin da su kan tsinci kansu a ciki, musamman daga jahohin da suka yi ƙaurin suna wajen samun matsalolin cin zarafi, sabanin shekarun baya da babu wuraren shigar da ƙara.

Shugabar ta kuma koka da yadda ƙasar ke tafiyar hawainiya wajen ƙwatar wa al’umma haƙƙinsu, inda ta bayyana cewa yanayin zamantakewa, da addini, da kuma al’ada na a matsayin wasu daga cikin abubuwan da kan haifar da cikas.

Grace Abim ta jaddada cewa yana da matuƙar muhimmanci doka ta yi halinta a kan duk wani mai laifi, ganin cewa matsalar cin zarafi ba ya la’akari da shekaru, ko jinsi, ko al’ada, ko addini, ko kuma matsayi, kodayake mata da ƙananan yara ne matsalar ta fi shafa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)