
Sanarwa daga ‘yan siyasa irin su Godswill Akpabio, wato shugaban majalisar dattijan Najeriya, shugaban kungiyar gwamnonin kasar kuma gwamnan jihar Gombe, Muhammad Inuwa Yahaya, tsohon mataimakin shugaban kasar, Atiku Abubakar, da sauransu, sun bayyana shi a matsayin wanda ya bayar da gudun mowa sosai ga ci gaban kasar.
Haka zalika tsoffin shugabannin kasar, Muhammadu Buhari da Goodluck Jonathan, da ibrahim Badamasi Babangida, sun aike da sakon alhinin rashin Mista Clark.
A ranar Litinin ne, Edwin Clasrk ya rigamu gidan gaskiya, a cewar sanarwar da iyalansa suka fitar jiya Talata.
An haifi marigayin rana 25 ga watan Mayun 1927 a kauyen Kiagbodo na ƙabilar Ijaw, da ke jihar Delta a Najeriya.
Ya kasance shugaban ‘yan ƙabilar ta Ijaw, kuma dan siyasa wanda ya taka rawar gani a fagen siyasar kasar.
Edwin Clark ya yi aiki da gwamnatocin mulkin soja na Gwamna Samuel Ogbemudia da shugaban ƙasa Janar Yakubu Gowon a tsakanin 1966 zuwa 1975.
A 1975, aka nada shi kwamishinan yada labarai na tarayya, wanda ya yi daidai da muƙamin ministan yada labarai a yanzu.
A lokacin Jamhuriya ta biyu ne aka zabe shi a matsayin Sanata a 1983 amma ya yi watanni uku kacal ne aka kujerar, sakamakon hamɓarar da gwamnatin Shehu Shagari da sojoji suka yi.
Ya kasance mai taimakon jama'a abin da ya sanya shi ma kafa wata gidauniya ta Edwin Clark Foundation, tare da samar da jami’ar Edwin Clark a yankin da ya fito a 2015.
Shigar sa siyasa ta fara ne a shekarar 1953 lokacin da aka zabe shi kansila na Bomadi. Daga baya ya shiga jam’iyyar fafutuka da ta kunshi ‘yan Najeriya da ‘yan Kamaru wato NCNC.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI