An tsare ƴan Najeriya akalla dubu 10 a ƙasashen ketare - Shettima

An tsare ƴan Najeriya akalla dubu 10 a ƙasashen ketare - Shettima

Mataimakin shugaban Najeriya Kashim Shettima ne ya bayyana haka a yayin gudanar da taron tattauna kan batun shige da fice karo na 10 a birnin Abuja a ranar Litinin da ta gabata.

Kodayake Shettima ya jinjina wa ƴan Najeriya da suka yi ƙaura zuwa ƙasashen ketare saboda gudunmawarsu wajen bunƙasa tattalin arzikin duniya, yana mai cewa, Najeriya ce ke kan gaba a jerin masu  aikewa da kuɗaɗe zuwa yammacin Afrika daga ketare.

Baya ga aikewa da kuɗaɗen zuwa gida, Shettima ya ƙara da cewa, ƴan Najeriya da ke ƙetare sun zama jakadun duniya da suka yi fice a ɓangarori da dama da suka haɗa da kimiya da fasaha da likitanci da wasannin motsa jiki da fasahar zane-zane da dai sauransu.

A cewarsa, ƙaura ba wai iya tsallakawa ba ce daga wata ƙasa zuwa wata, domin kuwa tana taka muhimmiyar rawa wajen ci gaban duniya, yana mai cewa, a shekarar 2022 kaɗai, ƴan Najeriya sun aika da kuɗin da ya kai dala biliyan 21.9 zuwa gida daga ƙasashen ƙetare, abin da ya yi daidai da kashi 64 na ɗaukacin kuɗaɗen da aka aiko zuwa yammacin Afrika a shekarar.

Wannan manuniya ce kan irin gagarumar gudunmawar ƴan Najeriya mazauna ƙetare a fannin bunkasa tattalin arziƙin kasar a cewar mataimakin shugaban na Najeriya.

Kodayake Shettima ya yi gargaɗi kan yawaitar kalubaalen da ke tattare da ƙaura, yana mai bayyana takaicinsa kan yadda Najeriya ta amshi ƴan kasar kimanin dybu 10 da aka dawo da su gida bayan sun aikata wasu laifuka masu nasaba da ƙarya dokokin shige da fice a kasashen duniya daban-daban.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)