Kakakin Rundunar Ƴan Sandan, ASP Ahmed Rufa’i wanda ya tabbatar da haka a yau Juma’a, ya ce an hana zirga-zirga a yankin daga ƙarfe 6 na safe zuwa 6 na yamma.
Rahotanni sun ce matasan sun ƙona shelkwatar jam’iyyar APC na Sabon Birni da kuma wata kotu, kana suka kutsa cikin rumbun ajiya ta ƙaramar hukumar, inda suka lalata takin zamani da ke ajiye a wurin.
An gudanar da jana'izar marigayin
Tuni aka gudanar da jana’izar sarkin Gobir Alhaji Isa Bawa bayan da iyalansa suka ɗebe tsammanin ganin gawarsa. An dai yi masa sallar ce ba tare da gawarsa ba wato Salatul Ga'ib.
Wannan ta faru ne bayan da ƴan bindigar suka hana gawarsa tare da ikirarin yi masa sutura a cikin daji.
Majiya daga iyalan Sarkin ta ce duk da ƴan bindigar sun kashe shi, sai da suka karɓi Naira miliyan 60 da babura guda 5 ɗin da suka buƙata a matsayin kuɗin fansa kafin su saki ɗansa mai suna Kabiru da suka kama su tare da mahaifin sa.
Kawo yanzu dai ana raɗe-raɗin cewa ɗan nasa Kabiru ya gamu da ruɗewar kwakwalwa sakamakon tashin hankalin da ya gamu da shi a cikin dajin.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI