An taƙaitawa ƴan Najeriya adadin kuɗaɗen da za su riƙa cirewa a kullum

An taƙaitawa ƴan Najeriya adadin kuɗaɗen da za su riƙa cirewa a kullum

Jaridar ta ce alamu na nuna cewa bankuna sun takaita abin da abokan hulɗarsu ke cirewa ta na’urar ATM zuwa Naira dubu 20 a kowace rana, koda kuwa mutum na da asusu daban daban a bankuna.

Matsalar ƙarancin takardun kuɗin ya ƙara yawaita ne a ‘yan kwanakin nan, duk da batun babban bankin Najeriya CBN na cewa bankunan ƙasar na da isassun kuɗin da za su iya fitarwa domin abokan huldarsu su cira, har ma ya yi gargaɗin ƙaƙaba musu takunkumai idan su ka ƙi yin biyayya.

Gwamnan CBN, Olayemi Cardoso ne ya bayyana haka a wajen taron liyafar cin abinci na shekara-shekara wanda Cibiyar Kula da Bankuna ta Najeriya (CIBN) ta shirya a Legas kwanan nan, kuma ya ba da tabbacin cewa bankin zai ci gaba da samar da kuɗaɗe don biyan bukatun ƴan ƙasa.

Ko a wata sanarwa mai ɗauke da sabbin ƙa’idoji da CBN ya fitar jiya Talata, bankin ya bayyana cewa ƴan Najeriya na da damar cirar kuɗi da bai wuce Naira dubu 100 ba a kowace rana, yayin da za su cire iya Naira dubu 500 a kowane mako.

Kana, masu sana’ar POS na da damar yin hada-hada da kuɗin da bai haura Naira miliyan 1.2 ba a kowace rana, amma duk da hakan ƴan ƙasar na fuskantar matsalar ƙarancin takardun kuɗi a hannunsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)