Ƴan ta'adda sun kashe sojojin Najeriya 27 a wani harin kwanton ɓauna

Ƴan ta'adda sun kashe sojojin Najeriya 27 a wani harin kwanton ɓauna

Rahotanni sun ce, maharan sun kai hari kan wani sansanin soji da ke garin Malam-Fatori a arewa maso gabashin jihar Borno, inda wani sojan da ya tsira ya ce an ɗauki sama da sa’o’i uku ana musayar wuta tsakaninsu da mayakan.

Mayakan Boko Haram da na ISWAP sun fi kai hare-hare a Borno, inda suke kai hari kan jami’an tsaro da fararen hula, abin da ya yi sanadin rayukan dubun dubatar mutane a yankin na arewa maso gabashin Najeriya.

Kamfanin dillancin labaran reuters ya ruwaito majiyoyin tsaro da mazauna yankin na cewa, wani kwamanda na cikin waɗanda aka kashe bayan da ‘yan kungiyar ta ISWAP suka kai farmaki kan bataliya ta 149 ta sojojin Najeriya da ke garin Malam-Fatori mai iyaka da Nijar.

Jihohin Arewa maso Gabashin Najeriya, sun jima suna fama da tashe-tashen hankulan masu dauke da makamai, abin da ya haifar da kalubale mai tarin yawa ga ayyukan jin kai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)