Ƴan sandan Najeriya sun yi watsi da rahoton Amnesty kan kisan masu zanga-zanga

Ƴan sandan Najeriya sun yi watsi da rahoton Amnesty kan kisan masu zanga-zanga

Rahoton ƙungiyar mai kwanan watan 28 ga watan Nuwambar 2024, ya zargi jami’an ƴan sandan ƙasar da kashe fararen hula aƙalla 24 a jihohi 6 na arewacin ƙasar.

Sai dai rundunar ƴan sandan ta bayyana rahoton a matsayin na ƙarya, kuma ba shi da tushe ballantana makama, haka zalika ta ce anyi shi ne don a ɓatanci ga  rundunar.

Rundunar ta kuma ce bayanan  da ta tattara game da zanga-zangar tsadar rayuwar ta watan Agustan da ya gabata, sun saɓa da zargin da ƙungiyar Amnesty ke yi.

Mai magana da yawun rundunar, Muyiwa Adejobi da yake zantawa da manema labarai yau Lahadi, ya ce sun haɗa tawaga ta musamman da za ta yi bincike kan rahoton.

Rundunar ta buƙaci ƙungiyar Amnesty da ta janye wannan rahoton domin ba shi da tushe, tare da shawartar ta da ta riƙa fitar da bayanai na gaskiya waɗanda za su haifar kwanciyar hankali da zaman lafiya tsakanin al’umma, baya ga buƙatar ta fito ta bata haƙuri.

A watan Agustan shekarar 2024 ne aka gudanar da zanga-zanga mai taken 'Endbadgovernance' a Najeriya, wadda ta haddasa asarar rayuka da dukiyoyi na gwamnati da wasu ɗaiɗaikun jama'a.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)