ƴan sandan Najeriya sun kama masu aikata muggan laifuka sama da 2700 a wata 1

ƴan sandan Najeriya sun kama masu aikata muggan laifuka sama da 2700 a wata 1

Kakakin rundunar ƴan sanda, Muyiwa Adejobi, wanda ya tabbatar da haka a wata sanarwa, ya ce an kama gungun da ake zargin da ya kunshi shugabansu Taimako Mato, John Danladi, Mohammed Munkail, Manasseh William da Muhammadu Haddi ɗauke da bindiga mai sarrafa kanta ta  PKT machine gun, guda ɗaya da kuma tarin harsasai da aburusai.

Adejobi ya ce shugaban gungun ƴan bindigan, Taimako Mato,  jami’in horar da yadda ake harba bindiga ane a wanin sansanin Boko Haram, wanda ke sayen haramtattun makamai yana sayarwa ta hannun mambobin kungiyarsa.

Ya kuma bayyana nasarar da rundunar ta yi ta kama mutane dubu 2 da ɗari 7 da 40 da ake zargi da aikata manyan laifuka da su ka hada da garkuwa da mutane, fashi da makami,  kisan kai da suran su.

 Rundunar ta kuma karɓi bindigogi 185 da harsasai da alburusai guda dubu huɗu da 87, babbura 111, ta kuma ceto mutane 129 da aka yi garkuwa da su.

A Najeriya, ana danganta safarar makamai da ayyukan ƴan ta’adda musamman ma a yankuna  arewacin ƙasar, inda kungiyoyi kamar Bko Haram da ƴan binidga ke cin karesu ba babbaƙa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)