Ɗan sanda ya dabawa wani wuka saboda ya hanashi cin hancin naira 200 a Yobe

Ɗan sanda ya dabawa wani wuka saboda ya hanashi cin hancin naira 200 a Yobe

Lamarin ya faruwa bayan faɗa tsakanin sufeton mai suna Mohammed Bulama da wanda aka hallaka Abdulmalik Pompomari.

Rahotanni sunce an kama sufeton da ake zargi da wannan aiki, kuma lamarin ya faru da misalin karfe 05:05 na yamma a Zango dake Damaturu a jihar Yobe dake arewacin Najeriya.

Jaridar dailytrust ta rawaito wata majiya na cewar sufeto Muhammad Bulama ya buƙaci naira 200 a hannun Abdulmalik, amma da ya hanashi sai kawai ya yi masa raunuka a tsakanin wuyansa da kirji, abinda ya kai ga mutuwarshi har lahira.

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar DSP Dungus Abdulkarim ya ce kwamishinan yan sandan Yobe Garba Ahmed, ya umarci a ƙaddamar da bincike kan wannan lamari.

Dungus ya kuma tabbatar da cewa tuni aka kama sufeton da ake zargi da aikata laifin domin bincike.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)