Ƴan sanda sun tseratar da mutum 18 daga harin masu garkuwa da mutane a Katsina

Ƴan sanda sun tseratar da mutum 18 daga harin masu garkuwa da mutane a Katsina

Wasu ƴan bindiga ne suka kai hari tare da buɗe wuta ga motoci 4 a kan babbar hanyar ta Funtua zuwa Gusau ranar 3 ga watan Janairu na 2024.

A wata sanarwa da rundunar ƴan sandan ta fitar yau Lahadi, mai magana da yawunta a jihar ASP Abubakar Sadiq ya ce sun dakile yunkurin ƴan bindigar na yin garkuwa da mutum 18.

Ƴan sandan sun kuma yi bata kashi da ƴan bindiga da suka sace shanu a Gidan Gada dake ƙaramar hukumar Kafur dake Katsina.

Baturen ƴan sandan yankin Kafur da Malumfashi ne ya jagoranci tawagarsa tare da bin sawun ƴan bindigar zuwa ƙauyen Fanisau inda aka yi musayar wuta tare da ƙwato dukkanin dabbobin da suka sace.

Kwamishinan ƴan sandan jihar CP Aliyu Abubakar Musa ya yabawa jami’an ƴan sandan da suka yi wannan aiki tare da miƙa buƙata ga alumma da su ƙara bada goyan baya ga jami’an tsaro, tare da basu bayanai da za su taimaka wurin tabbatar da zaman lafiya a yankunansu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)