Ƴan sanda sun tarwatsa masu zanga-zanga da barkonon tsohuwa a Abuja.

Ƴan sanda sun tarwatsa masu zanga-zanga da barkonon tsohuwa a Abuja.

Masu zanga-zangar sun taru ne da safiyar yau talata a kasuwar mai cike da hada-hada inda suka sha harbin barkonon tsohuwa daga jami'an ƴan sanda.

Wasu daga cikin kungiyoyin fararen hula ne dake da alaƙa da zanga-zangar da aka yi ta kawo ƙarshen gurbataccciyar gwamnati ne suka fito a yau da ake bikin cika shekara 64 da samun ƴancin kan Najeriya.

Zanga-zangar ta 1 ga watan Oktoba da aka yiwa laƙabi da #FearlessInOctober, ba ta ɗauki hankali ba kamar yadda ta farkon watan Agustan da ya gabata ta yi.  

An fara zanga-zangar ne a wasu sassan Najeriya kamar Lagos da babban birnin tarayyar ƙasar Abuja, kuma tana da nufin nuna ƙin amincewa da halin da ake ciki dangane da tsadar kayan abinci da man fetur da ma hauhawar farashin sauran kayayyaki da ake fuskanta a ƙasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)