Ƴan sanda sun kame masu gangamin tunawa da zanga-zangar EndSARS a Lagos

Ƴan sanda sun kame masu gangamin tunawa da zanga-zangar EndSARS a Lagos

Tun da safiyar yau Lahadi ɗimbin matasa suka yi dafifi a dai dai shingen karɓar kuɗaɗe na hanyar zuwa anguwar Lekki a jihar ta Lagos don tunawa da ranar ta 20 ga watan Oktoban 2020.

Rahotanni sun ce galibin matasan sun riƙa rera waƙoƙi yayinda wasunsu ke riƙe da kwalaye masu rubutun alawadai da cin zarafin shekaru 4 da suka gabata, gabanin jami’an ƴan sanda su tarwatsa su tare da kame kaso mai yawa.

Yayin zanga-zangar ta wancan lokaci bayanai sun nuna yadda ɗimbin matasa suka rasa rayukansu bayan zargin cewa Sojojin da aka girke a wajen sun buɗe musu wuta.

Shekaru 4 kenan da faruwar wannan lamari, har kawo yanzu ana ci gaba da taƙaddama kan ainahin adadin mutanen da suka rasa rayukansu a gangamin wanda a lokacin matasan ke neman kawo ƙarshen cin zarafin da sashen rundunar ƴansanda ta SARS mai yaƙi da ayyukan fashi da makami ke yi a ƙasar.

Sai dai bayan da zanga-zangar ta juye zuwa tarzoma Gwamnan jihar ta Lagos Babajide-Sanwo-Olu ya sanya dokar taƙaita zirga-zirga a wancan lokaci amma duk da haka matasan da ke shingen na Lekki suka ci gaba da zama a wajen lamarin da ya tilasta girke dakarun Soji.

Ƙungiyar Amnesty International ta bayyana cewa a nan take Sojojin Najeriya sun hallaka mutane 12 sai dai gwamnatin Najeriya ta wancan lokaci ta musanta batun kisan ko da mutum guda haka zalika rundunar Sojin ƙasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)