Ƴan sanda sun kama masu sayar wa ƴan Boko Haram babura a jihohin Neja da Kaduna

Ƴan sanda sun kama masu sayar wa ƴan Boko Haram babura a jihohin Neja da Kaduna

A lokacin da mataimakin sifeta janar na ƴan sandan Najeriya da ke kula da shiya ta 7 AIG Benneth Igweh, ke ganawa da manema labarai, ya ce sun samu nasarar kama Shamsuddeen Yunusa da Zaharadeen Saidu da kuma Mustapha Haruna ne a garin Suleja da ke jihar Nijar, sakamakon bayanan sirrin da suka samu.

Ya ce mutanen sun kware wajen yin kasuwanci da gyaran baburan da aka sato, kuma suke sayar da su ko bada haya ga masu aikata laifuka, ciki har da wasu da ake zargin ƴan Boko Haram ne da ke kai hare-hare a sassan jihohin Neja da Kaduna.

A wani yunkuri na daƙile ayyukan ta’addanci a birnin Abuja da jihar Neja, an tura jami’an shiyya ta 7 zuwa karamar hukumar Suleja ta jihar Neja, inda suka yi nasarar cafke wasu mutane uku da ake zargi, an samu nasarar kwato babura 22 da makullai iri-iri da kuma wayoyin da aka sato.

Da dama daga cikin ƴan ta'adda a Arewacin Najeriya suna amfani da babura wajen kai hare-hare da kuma garkuwa da mutane.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)