Binciken wanda jaridar Daily Trust da ake wallafa a Najeriya ta gudanar, ya nuna cewa jami’an ƴan sanda sun gamu da ajalinsu ne a hannun ƴan bindiga da mayakan Boko Haram da ƴan daba da masu mashi da makami da kuma ƴan ƙungiyar asiri.
Rahoton ya ce a shekarar 2023 kadai, jami’an ƴan sanda 118 masu mukami daban daban ne aka kashe, sannan aka sake kashe wasu 111 a watannin goman farkon wannan shekarar a Najeriya.
Na baya-bayan dai shi ne kisan ASP Augustine Osupayi da ke aiki da rundunar ƴan sanda reshen jihar Lagos, wanda aka kashe a watan Oktoban da ya gabata, a lokacin da shi da tawagarsa suka yi ƙoƙarin dakatar da wasu ɗaukar doka a hannunsu a yankin Agage.
Wasu ƴan sanda da jaridar ta zanta da su kan lamarin, sun ce hakan ba zai sa su ƙasa a gwiwa ba wajen gudanar da aikinsu na kare al’umma ƙasar.
To sai dai rundunar ƴan sandan Najeriya batace komai ba kan wannan bincike, duk da dai wata majiya ta tabbatarwa da jaridar cewa sifeta janar na ƴan sandan Najeriya ya bada umarnin gudanar da bincike kan kisan ƴan sandan da ake samu a baya-bayan nan.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI