
Hukumar ta tattara korafe-korafe 427,606 a cikin watan Oktoba, wanda ya nuna karuwar kashi 27 cikin 100 na korafe-korafe idan aka kwatanta da watan Satumba.
Da yake gabatar da sabon rahoton, babban mai baiwa hukumar shawara, Hilary Ogbonna, ya ce watan Oktoba ne aka fi samun rahoton yawan kashe-kashe da sace-sace a Najeriyar.
Mista Ogbonna ya bayyana cewa fashewar wata tankar dakon man fetur a jihar Jigawa wanda ya yi sanadin mutuwar mutane 167 na daga cikin adadin rahoton mutanen da suka mutu a watan Oktoba da aka sanya.
Sakataren zartarwa na hukumar, Tony Ojukwu, ya ce karuwar adadin da aka bayar na nuni da cewa ba za a iya kwatanta yadda ake take hakkin dan adam a sassan kasar ba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI