A cewar Amnesty, matsalar ɗaukar doka a hannu na ci gaba da zama ruwan dare a sassan Najeriya, matsalar da ƙungiyar ke cewa na da nasaba da rawar da mahukunta ke ɗauka ta gaza baiwa rayukan jama’a kariya.
Cikin wani rahoto da ƙungiyar ta fitar a yau Litinin ɗauke da sa hannun shugaban a Najeriya Isa Sunusi, Amnesty International ta ce baya ga matsaloli masu alaƙa da ta’azzarar cin hanci da rashawa da rashin hukuncin adalci tsakanin shugabanni, akwai kuma yadda shugabanni ko malaman addinai ke taka muhimmiyar rawa wajen tunzura jama’a don ɗaukar doka a hannu yayin faruwar batutuwa masu alaƙa da ɓatanci.
Alƙaluman da Amnesty ta tattaro daga watan Janairun 2012 zuwa Agustan 2023 ya nuna yadda tarin mutane suka rasa rayukansu a hannun jama’a sakamakon tuhumarsu da laifuka masu alaƙa da ko dai aikata tsafi, ko maita ko ɓatanci koma sata a wasu lokutan har ma ƙananun laifi.
Amnesty ta bayyana rashin gamsuwa da matakan da mahukuntan Najeriya ke bi wajen ladabtar da mutanen da suka yi irin wannan kisan kai, wanda ƙungiyar ke cewa a lokuta da dama sukan tsira ba tare da an hukunta su ba.
A cewar Amnesty a tsakanin shekarun 10 akwai bayanan hukumomin tsaron Najeriyar 363 da ke nuna yadda mutane 555 suka rasa ransu a hannun jama’a sakamakon tuhumarsu da laifuka mabanbanta.
Amnesty ta ce a cikin wannan mutane akwai 57 da aka yiwa kisan nan take lokacin da aka far musu sai kuma 32 da aka ƙone ƙurmus kana 2 da aka birne da ransu sai kuma 23 da aka riƙa azabtar da su har suka rasa rayukansu.
Amnesty ta bayyana cewa matsalar ta irin wannan kisa ta hanyar ɗaukar doka a hannu na ci gaba da faruwa a yankunan karkara waɗanda ba a fiya shigar da rahoton gaban mahukunta ba.
Amnesty International ta ce a yankin Arewacin Najeriya an fi samun matsalar ta aikata kisa bayan ɗaukar doka a hannu bisa zargin mutane da aikata ɓatanci yayinda a kudancin ƙasar aka fi yin wannan aika-aika sakamakon zargin mutane da aikata tsafi ko maita ko kuma Sata.
A jumulla yankin Arewacin Najeriya ya fi samun yawan kisa ta hanyar ɗaukar doka a hannu inda yankin arewa maso yamma ke da mutane 100 da suka fuskanci irin wannan kisa a tsawon shekarun 10 sai arewa maso gabas da mutane 26 kana tsakiyar Arewa da mutane 42.
Yankin kudancin Najeriyar wanda shi ne mafi ƙarancin samun kisan ta hanyar ɗaukar doka a hannu, alƙaluman na Amnesty ya nuna yadda mutane 82 a kudu maso kudu suka rasa rayukansu saboda wannan matsala sai 43 a kudu maso gabas kana 98 a kudu maso yammacin ƙasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI