
Hukumar da ke sa ido kan hada-hadar kuɗaɗe tsakanin bankunan Najeriya ce ta fitar da rahoton, wanda ya ce kimanin Dala miliyan 34.8 kwatankwacin Naira biliyan 52 ne ‘yan Damfara suka yashe daga bankuna a Najeriya cikin hekarar 2024 da ta gabata, lamarin da ya nuna ƙaruwar matsalar da ninki 4, idan aka kwatanta da Naira biliyan 11.6 da aka tafaka hasararsu a shekarar 2020.
Rahoton ya ƙara da cewar duk da Naira biliyan 52 da aka rasa a bara, ba ƙaramar sa’a aka yi ba cikin shekarar ta 2024, la’akari da cewar riƙaƙƙun ‘yan Damfarar da aka fi sani da ‘yan Yahoo a Najeriya sun yi aniyar sace Naira biliyan 86.4 ne daga bankuna, amma suka gaza aiwatar da mugun nufin nasu.
Daga cikin hanyoyin da ‘yan damfarar suka fi amfani da su a Najeriyar dai akwai buɗe asusun ajiyar kuɗaɗe ta hanyar satar bayanan abokan hulɗar bankunan da basu ji basu gani ba.
An fusanci ƙaruwar matsalar ‘yan damfarar ta Yahoo a Najeriyar ne a daidai lokacin da ake samun bunƙasar hadar kuɗaɗe ta bankuna a matakai daban daban ba tare da yawaitar gamuwa da cikas ba.
A halin da ake ciki an samu nasarar ƙwato miliyoyin kuɗaɗe daga hannun ‘yan damfara, yayin da kuma ake gudanar da bincike kan ma’aikatan bankunan da ake tuhumar suna da hannu cikin ta’asar da aka tafka.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI