An sake ƙara farashin litar man fetur a gidajen NNPCL a Najeriya

An sake ƙara farashin litar man fetur a gidajen NNPCL a Najeriya

Wannan sabon ƙari na zuwa makwanni 3 da ƙarin da kamfanin NNPCL yayi. A ranar 9 ga watan Octoba 2024 kamfanin mai ya ƙara farashin lita zuwa Naira 1,030 a babban birnin tarayyar Najerya Abuja, sai kuma farashin ya tashi a jihar Lagos daga 897 zuwa Naira 998.

Rahotann daga gidajen mai na NNPC sun tabbatar da cewa a Lagos farashin na kaiwa har 1,025 kan kowaccce lita.

Ƙarin farashin na zuwa yayin da ƴan Najeriya suka ƙauracewa sayan mai saboda tsadar da yayi tare da samun raguwar ababan hawa dake sufuri a biranan ƙasar.

Har wa yau ƙarin na zuwa yayin da wasu Alƙaluman da hukumar kula da albarkatun ruwa da kuma ƙarƙashin ƙasa a Najeriya suka nuna cewar an samu raguwar man da ake sha daga lita miliyan 60 a kowacce rana zuwa lita miliyan 4 da dubu 500 a 20 ga watan Agustan 2024.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)