Ƴan Najeriya sun biya fansar sama da naira tiriliyan 2 cikin watanni 12- NBS

Ƴan Najeriya sun biya fansar sama da naira tiriliyan 2 cikin watanni 12- NBS

NBS da ta tattara wannan alƙaluman bayan binciken da ta gudanar kan halin da ake ciki a yankunan da matsalolin ƴan bindiga suka fi ta’azzara ta ce ƴan Najeriyar sun bayar da adadin kuɗin ne a tsakanin watan Mayun shekarar 2023 zuwa Aprilun 2024.

Rahoton da NBS ta wallafa jiya Talata, ta ce bincikenta ya gano yadda kashi 65 na mutanen da ƴan uwansu suka shiga hannun ƴan bindiga a wannan ɗan tsakani na watanni 12 suka biya fansa don kuɓutar da ahalin na su daga hannun ɓatagarin.

NBS ta ce jumullar fansar da ƴan bindigar suka karɓa a watannin 12 ya kama naira tiriliyan 2 biliyan 231 da miliyan 772 da dubu 563 da ɗari 507 daga cikin tiriliyan 2 da biliyan 670 da miliyan 693 da suka nema.

Alƙaluman na NBS sun ce ƴan bindiga sun yi garkuwa har sau miliyan 2 da dubu 235 da 954 a tsawon wannan lokaci ko da ya ke hukumar ta ce matsalar ta fi ƙamari a yankunan karkara fiye da birane.

Rahoton ya ce yankin arewa maso yammacin Najeriyar shi ne kan gaba a samun wannan matsala ta garkuwa da mutane biye da yankin tsakiyar Arewar kana yankin kudu maso gabashi.

Hukumar ta NBS ta ce kashi 80.5 na waɗanda suka faɗa komar ƴan bindigar sun kai batun ga hukumar ƴan sansa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)