A cewar wasu alkaluma da hukumar kula da shigi da fice ta Amurka ICE ta fitar a watan Nuwanbar shekarar da ta gabata, sun nuna cewar akwai bakin haure sama da miliyan ɗaya da dubu dari 445 da dari 549 da ke zaune a ƙasar ba bisa ƙa’ida ba, ciki kuwa harda ƴan Najeriya dubu 3 da dari 690.
To sai dai a wasu sabbin alkaluma da hukumar ta fitar, su nuna cewa akai ƙarin wasu ƴan Najeriya dubu ɗaya da dari 454 da ake tsare da su, kuma ake shirin maida su gida.
Hukumar ta ce daga cikinsu akwai 772 da ke jiran hukunci wasu kuma an yanke musu, bayan samunsu da laifuka daban daban ciki har da na saɓawa ƙa’idar shiga ƙasar.
Duk da cewa ma’aikatar kula da harkokin wajen Najeriya bata ce komai kan lamarin ba, amma hukumar da ke kula da ƴan ƙasar da ke zaune a ƙasashen ƙetare, ta ce tuni ta samar da wani kwamiti da zai kula da lamarin.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI