Babu cikakken bayani kawo yanzu na musabbabin matsalar sadarwar da ake fuskanta a ƙasar.
To sai dai hakan na faruwa biyo bayan shugaban kamfanin sadarwa na MTN a Najeriya Karl Toriola ya yi kira ga gwamnatin ƙasar da ta ƙara kudin waya inda ya ce rashin yin haka zai kawo mummunar illa.
Ita ma hukumar sadarwa ta Najeriya NCC ta ga baiken kamfanin sadarwa na Starlink bisa ƙara kuɗin data ba tare da an amince masa ba, inda suka bayyana haka a matsayin karya dokokin hukumar.
NCC ta ce kamfanonin sadarwa dake amfani da tauraron ɗan adam sun ƙara kuɗin data.
A tattaunawar da RFI ta yi da wasu ƴan Najeriya sun nuna damuwa kan wannan matsala.
Gaskiya a yanzu data ba ta daɗewa kwata-kwata, yawancin ina sayan na kwana 2 amma yanzu a rana ɗaya take ƙarewa –Maryam Yunus
To a gaskiya al’amarine mara daɗi duba da yadda wasu abubuwa suke faruwa a Najeriya –Aminu Nasir Jasawa
Matsalar da nake kallo a wannan abun shine, datar da ake amfani da ita a yanzu tana karewa da wuri saboda a baya da babu manhajoji kamar TikTok da Youtube. Haka kuma akwai banbancin wayoyi domin na yanzu suna da saurin shanye data –Abu Sha’aban Communication
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI