Ƴan Najeriya na fama da matsalar kwakwalwa saboda tsadar rayuwa

Ƴan Najeriya na fama da matsalar kwakwalwa saboda tsadar rayuwa

Wasu masana kiwon lafiyar bil Adama a Najeriya Aisha Bubah da Jecinta Egbim suka bayyana haka sakamakon irin halin kuncin da jama'ar kasar suka samu kansu a ciki.

Rahotan ya ce cibiyoyin lafiyar Najeriya sun samu ƙarin sama da kashi 200 na masu fama da irin waɗannan matsaloli a Najeriya.

Hukumar lafiya ta Duniya ta ce mutane sama da dubu 720 ke kashe kansu da kansu kowacce shekara a duniya saboda shiga irin wannan yanayi, kuma kashi 77 daga cikinsu na fitowa ne daga kasashe matalauta da kuma masu tasowa irin Najeriya.

Masanan sun ce Najeriya ce gaba wajen samun mutanen da yanayin rayuwa ke shafar lafiyar kwakwalwarsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)