Najeriya mafi yawan jama’a a nahiyar Afrika na fama da matsalar tsadar rayuwa da hauhawar farashin kayaki wanda ya sanya al’ummarta tsunduma zanga-zangar adawa da manufofin gwamnati da suka takure jama’a cikin watan Agustan da ya gabata.
Rahoton haɗakar tsakanin ƙwararru daban-daban daga hukumomin majalisar da suka ƙunshi FAO da WFP da kuma takwarorinsu na Najeriya ya nuna yadda za a samu ƙaruwar kashi 1 bisa 3 na mutanen da suka yi fama da ƙarancin abinci a bana, idan an kwatanta da waɗanda za su fuskanci matsalar a baɗi.
Wani ƙaramin yaro da yunwa ta galabaita. (File | AP)Masanan sun alaƙanta matsalar ƙarancin abincin da ƴan Najeriyar miliyan 33 za su faɗa a baɗi kan manufofin shugaban ƙasar Bola Tinubu da suka tsawwala rayuwa wanda ya sanya manoma da dama haƙura da gonakinsu a bana.
Wasu daga cikin matakan acewar rahoton sun ƙunshi karya darajar takardar kuɗin ƙasar a lokuta da dama da kuma janye tallafin man fetur wanda ya jefa jama’ar ƙasar a wahala.
Rahoton ya ce za a ga matsalar ƙarancin abinci a jihohin Najeriyar 26 da Abuja fadar gwamnati wadda za ta shafi mutanen miliyan 33 da dubu 100 matsalar da za ta ta’azzara a watan Agustan baɗi da adadin mutanen mafi yawa idan an kwatanta da mutum miliyan 24 da dubu 800 da suka fuskanci makamanciyar matsalar a bana.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI