Ƴan Najeriya miliyan 32 na fama da matsananciyar yunwa - rahoto

Ƴan Najeriya miliyan 32 na fama da matsananciyar yunwa - rahoto

Wannan alƙaluma na mutum miliyan 31 da 800 a cewar shirin abinci na Majalisar Dinkin Duniya WFP ya zarta adadin mutanen da suka faɗa baƙar yunwa a irin wannan lokaci a bara da ya kai mutum miliyan 18 da dubu 600.

Wasu bayanan haɗin gwiwa da hukumomin ƙasa da ƙasa na abinci da lafiya da kuma na agaji suka fitar a yau Laraba, sun ce halin matsananciyar yunwar da ake ciki a Najeriyar lamari ne mai tayar da hankali matuƙa.

A cewar sassan matsalar tsaro ta hana manoma da dama iya gudanar da harkokinsu na noma, lamarin da ya hadasa ƙarancin abincin, yayinda a ɓangaren guda hauhawar farashi ta hana mutane iya sayen nau’ikan abincin da akan shigar ƙasar daga ƙetare.

Ƙungiyoyin sun ce hatta matakin gwamnatin Najeriyar na cire tallafin man fetur ya taka muhimmiyar rawa wajen haddasa matsalar ƙarancin abincin da kuma tsadarsa ta yadda iyalai da dama basa iya ci su ƙoshi koma basa iya cin abincin kwata-kwata.

WFP da ƙungiyar agaji ta Jamus GIZ da kuma Global Alliance da ke sanya idanu kan hada-hadar abinci mai gina jiki a ƙasashe sun ce wannan matsala ta jefa rayuwar miliyoyin mata da ƙananan yara a haɗari cikin ƙasar ta Najeriya mafi yawan jama’a a Afrika.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)