Yanzu haka farfesa Usman, wanda shi ne mutun na farko da ya kai matakin farfesa a ɗaukacin yankin Igbo, ya shiga sahun limamai guda uku da ake da su da ke jagorantar salla a Masallacin na Abuja.
Farfesa Usman zai riƙa taimaka wa farfesa Ibrahim Maƙari da farfesa Muhammad Kabir wajan jagorantar sallar Juma'a da sauran salloli biyar na kullum, yayin da limami na huɗu, wato Sheikh Ahmad Onilewura daga yankin kudu maso yammacin Najeriya ke fama da rashin lafiya, abin da ya sa ya ɗauki dogon lokaci bai jagoranci sallah ba a Masallancin.
Farfesa Ilyas Usman © Abuja National MosqueA taƙaice dai, yanzu wannan Masallacin da aka gina shi tun shekarar 1984, na da limamai ratibai guda uku da suka haɗa farfesa Usman, sannan a gefe guda, akwai farfesa Shehu Ahmad Sa'id Galadanchi wanda ke a matsayin shugaban limaman baki ɗaya.
Tuni Ƙungiyar Musulmai ta Ƴan Ƙabilar Igbo ta Najeriya (SEMON) ta yi lale marhabin da wannan naɗin da aka yi wa farfesa Usman, inda ta yi masa addu'ar dacewa da kuma ƙarfin ɗaukar nauyin da aka rataya masa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI