A rahoton da Jaridar ta The Cable ta wallafa ta ce wata majiya a fadar shugaban Najeriyar Bola Tinubu ta tabbatar mata da yadda shugaban ya amince kamfanin mai na NNPCL ya dakatar da sanya ribar da ake hasashen za a samu ta shekarar 2024 tare da amfani da ribar da ya samu ta 2023 domin tallafawa sha’anin na man fetur.
Rahoton ya ce kamfanin man ƙasar ne ya kokawa Tinubu kan yadda cire tallafin mai ya shafshi tare da hadddasa masa tsaiko wurin shiga da fitar kuɗaɗe.
Tallafin mai
Kamfanin ya faɗawa shugaban ƙasa cewar a yanzu ba zai iya shigar da harajin da yake tarawa ba cikin asusun gwamnatin tarayya saboda batun tallafin na man fetur.
Wani hasashen kamfanin NNPCL da jaridar the Cable ta ce ta gani ya nuna yadda aka yi kiyasin kuɗin tallafin man fetur da za’a biya daga watan Agustan 2023 zai kai Tilriliyan 6 da miliyan 884 a Disambar 2024. Wannan zai sa kamfanin mai na ƙasar gaza shigar da Naira tiriliyan 3 da miliyan 987 a asusun gwamnatin tarayya.
To sai dai jaridar ta ce bata tabbatar da adadin ribar da aka amince kamfanin ya dakatar da shigarwa ba a asusun gwamnatin tarayya.
A bisa al’ada ana shigar da ribar da kamfanin mai ke hasashen zai samu a duk wata a asusun gwamnatin tarayya tare da kasaftawa tsakanin gwamnatin tarayya da jihohi da kuma kananan hukumomi sai kuma a kara aikewa da ragowar ribar da aka samu duk karshen shekara bayan kididdige adadin baki ɗaya.
Ribar NNPC
Kamar yadda dokar man fetur a Najeriya ta tanada an wajabtawa kamfanin mai na Najeriya shigar da haraji da ribar da ya samu a a duk shekara.
To sai dai kawo yanzu babu wani martani daga gwamnatin tarayya tun bayan wallafa wannan rahoto da jaridar ta yi, kuma babu wani bayani kan tasirin da hakan zai yi ga alummar Najeriya daidai lokacin da aka fara fuskantar dogayan lyuka agidajan mai ƙasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI