Mai magana da yawun rundunar ƴan sandar Prince Olamuyiwa Adejobi shine ya tabbatar da wannan labari, inda yake cewa,
"Haƙiƙanin gaskiya an ceto su ta hanyar amfani da dabarun aiki da ƙwarewa. Muna godiya ga jami'an tsaro da mazauna yankin da lamarin ya faru, da kuma ofishin mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan sha'anin tsaro bisa jajircewarsu".
Rundunar 'yan sandan Nijeriyar ta kara da cewa an kuɓutar da ɗaliban kiwon lafiyar aƙalla 20 da 'yan bindiga suka yi garkuwa da su a jihar Benue da ke tsakiyar ƙasar.
Adejobi ya kuma tabbatar da hakan ne a ranar Asabar kamar haka,
"Muna tabbatar muku cewa an sako 'yan'uwanmu ɗaliban kiwon lafiya 20 maza da mata da ma sauran wasu 'yan Nijeriya ranar Juma'a, 23 ga watan Agusta waɗanda aka yi garkuwa da su a dajin Ntunkon da ke jihar Benue," in ji Mista Adejobi.
An yi garkuwa da daliban ne, waɗanda ke cikin motocin bas guda biyu a ƙaramar hukumar Otukpo ta jihar Benue a makon jiya akan hanyarsu ta halartar wani taro a jihar Enugu daga birnin Jos babban birnin jihar Filato.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI